﻿Ayuba.
25.
Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa, 
“Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa; yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama. 
Za a iya ƙirga rundunarsa? A kan wane ne ba ya haska haskensa? 
Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki? 
In har wata da taurari ba su da tsarki a idanunsa, 
mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah!” 
