﻿Zabura.
3.
Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom. Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni! 
Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” Sela 
Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina. 
Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela 
Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni. 
Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba. 
Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye. 
Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela 
