﻿Zabura.
82.
Zabura ta Asaf. Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”. 
“Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? Sela 
Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya. 
Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye. 
“Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya. 
“Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne. 
Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.” 
Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne. 
