﻿Zabura.
87.
Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce. Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki. 
Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub. 
Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke Ya birnin Allah, Sela 
“Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ” 
Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.” 
Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa, “An haifi wannan a Sihiyona.” Sela 
Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.” 
