﻿Zabura.
102.
Addu’ar mutum mai shan wahala. Sa’ad da ya rasa ƙarfi ya kuma yi makoki a gaban Ubangiji. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka. 
Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni sa’ad da nake cikin damuwa. Ka juye kunnenka gare ni; sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri. 
Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi; ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta. 
Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa; na manta in ci abinci. 
Saboda nishina mai ƙarfi na rame na bar ƙasusuwa kawai. 
Ni kamar mujiyar jeji ne, kamar mujiya a kufai. 
Na kwanta a faɗake; na zama kamar tsuntsun da yake shi kaɗai a kan rufin ɗaki. 
Dukan yini abokan gābana suna tsokanata; waɗanda suke mini ba’a suna amfani da sunana yă zama abin la’ana. 
Gama ina cin toka a matsayin abincina ina kuma gauraye abin sha nawa da hawaye 
saboda fushinka mai girma, gama ka ɗaga ni sama ka yar a gefe. 
Kwanakina suna kamar inuwar yamma; na bushe kamar ciyawa. 
Amma kai, ya Ubangiji, kana zaune a kursiyinka har abada; sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai. 
Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona, gama lokaci ne na nuna alheri gare ta; ƙayyadadden lokacin ya zo. 
Gama duwatsunta suna da daraja ga bayinka; ƙurarta kawai kan sa su ji tausayi. 
Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji, dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka. 
Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona ya kuma bayyana a ɗaukakarsa. 
Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi; ba zai ƙyale roƙonsu ba. 
Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa, cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji, 
“Ubangiji ya duba ƙasa daga wurinsa mai tsarki a bisa, daga sama ya hangi duniya, 
don yă ji nishe-nishen ’yan kurkuku yă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.” 
Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona yabonsa kuma a Urushalima 
sa’ad da mutane da mulkoki suka tattaru don su yi wa Ubangiji sujada. 
Cikin rayuwata, ya karye ƙarfina; ya gajartar da kwanakina. 
Sai na ce, “Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah; shekarunka suna bi cikin dukan zamanai. 
A farkon fari ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne. 
Za su hallaka, amma za ka ci gaba; duk za su tsufe kamar riga. Kamar riga za ka canja su za a kuwa zubar da su. 
Amma kana nan yadda kake, kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba. 
’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka; zuriyarsu za su kahu a gabanka.” 
