﻿Zabura.
111.
Yabi Ubangiji. Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro. 
Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu. 
Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, adalcinsa kuma zai dawwama har abada. 
Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma. 
Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa; yakan tuna da alkawarinsa har abada. 
Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa, yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai. 
Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya; dukan farillansa abin dogara ne. 
Tsayayyu ne har abada abadin, ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya. 
Yana ba da ceto ga mutanensa; ya kafa alkawarinsa har abada, tsarki da banrazana ne sunansa. 
Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima; dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau. Gare shi ne madawwamin yabo. 
