﻿Zabura.
113.
Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji. 
Bari a yabi sunan Ubangiji, yanzu da har abada kuma. 
Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, a yabi sunan Ubangiji. 
Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai, ɗaukakarsa a bisa sammai 
Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu, Wannan mai zama a kursiyi can bisa, 
wanda yake sunkuya yă dubi sammai da duniya? 
Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka; 
ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu. 
Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji. 
