﻿Zabura.
129.
Waƙar haurawa. Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce, 
sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba. 
Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi. 
Amma Ubangiji mai adalci ne; ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye. 
Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya. 
Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma; 
da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa. 
Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.” 
