﻿Zabura.
134.
Waƙar haurawa. Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji. 
Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki ku kuma yabi Ubangiji. 
Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa, ya albarkace ku daga Sihiyona. 
